Ginsau HealthNetwork (GHN).
Saturday, February 15, 2020
Monday, February 3, 2020
Yadda zamu kaucewa kamuwa da ciwon daji (Cancer)
![]() |
| Aliyu Abubakar | |
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ware 4 ga watan Fabarairu 2020, domin wayar da kan Al'umma kan illar ciwon daji (cancer), sakamakon 'karuwar yaduwar jinyar da ake samu a duk shekara, Hukumar lafiyar ta baiyana cewa a shekarar 2018 a 'kalla mutane sama miliyan 18 ne a duniya suka kamu da ciwon daji (cancer), kuma kimanin mutane miliyan 10 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar cutar.
Ciwon daji (cancer) cutace dake faruwa sakamakon gurbacewar ƙ'kwayoyin halittu (cells) a jikin dan-Adam ko kuma samuwar matsala cikin 'kwayoyin halittun mutum na gado (DNA), wadda take yaduwa daga sashe zuwa sashe tare da karya duk wata kafa da ta shiga, kuma masana kiwon lafiya sun tabbatar da cewa, kaso 90 zuwa 95 cikin 100 suna kamuwa ne da cutar a sakamakon al'amurran zamantakewar su, inda ragowar kaso 5 zuwa 10 ke kamuwa da cutar a sakamakon gado tun daga iyaye da kakanni.
Alamomin ciwon daji (cancer)
alamomin da mutum zai gane cewa yana dauke da ciwon daji (cancer) sun hada da:
• Yawan tari mai tsayi
• Zubar da jini ba tare da wani dalili ba
• Bayyanar tsuro ko 'kari a jikin mutum
• Ramewar jiki da yawan kasala
• Yawan ciwon ciki musamman alokacin al'ada ga mata
• Rashin warkewar ciwo
• Amai, fitsari ko kashi mai jini a ciki
• Yawan tsugunno batare da cin abinci mai yawa ba
• Zubar jini ta hanci
Dazarar mutum ya fuskanci daya daga cikin wadannan alamomin ya gaggauta zuwa asibiti don ganin likita domin shawo kan cutar tun tana matakin farko, saboda ciwon daji nada wuyar sha'ani idan har ba'ayi saurin daukar mataki akansaba a matakin farko.
Abubuwan dake janyo ciwon daji (cancer)
• Shan sigari
• Tara te'ba ko 'kiba
• Rashin cin lafiyayyen abinci
• Rashin motsa jiki
• Hasken Rana
• Tsufa
• Gado
• 'kwayoyin cutar bakteriya da kuma virus
• Mu'amala da abubuwan da suka shafi chemicals
• Cin nau'ikan abinci ko abin sha dake dauke da sinadarin 'Nitrite' da sauransu
Sassa/Bangarorin da ciwon daji ke kamawa a jikin dan-Adam
Ciwon daji (cancer) yakan kama sassan jiki da suka hada da:
• Huhu
• Hanta
• 'Kwayoyin 'kwan halittar mata (overies)
• Bakin mahaifa
• Ido
• Mama
• Hanji
• Fata
• Prostate gland
• Jini, da kuma
• 'Kwa'kwalwa
Hanyoyin kariya daga kamuwa da ciwon daji (cancer) da kuma hanyoyin maganceta bayan kamuwa da cutar
• Cin abincin mai lafiya
• 'Kauracewa shan sigari da kuma barasa
• Motsa jiki
• Shan magungunan cutar bayan kamuwa da it's bisa sahalewar likita
• Samun isasshan bacci
• 'Kauracewa shiga rana sosai
• Yin rigakafin 'kwayoyin cutar virus ko bakteriya dake haifar da ciwon daji irinsu HPV da kuma Hepatitis B
• Amfani da sinadarin vitamin D
• 'Kone tsiron ciwon daji (chemotherapy) yayin baiyanarsa ko kuma cire tsiron gaba daya ta hangar tiyata.
Wadannan sune kadan daga cikin hanyoyin kariya daga kamuwa daga wannan cutar, kuma koda mutum yakamu da ita idan yana bin wadannan matakan to bazatayi wani tasiri na a zo a gani a jikinsaba, yana dakyau ga maza da mata da suka manyanta zuwa asibiti lokaci bayan lokaci domin tantance lafiyarsu kan wannan jinya.
Allah ya 'Kara mana lafiya
#WayarDaKai
#MuYakiCiwonDaji
#CancerDayAwareness
#4th_Feb_2020
©GHN
Sunday, January 26, 2020
Jinyoyin da mutane ke kamuwa dasu daga Dabbobi (Zoonotic Diseases)
![]() |
| Nura Idris | |
Dabbobi na taka muhimmiyar rawa a rayuwar mu musamman ta bangaren samar da nishadi da kuma kasancewar wasu daga cikinsu abinci garemu, sai dai a wasu lokutan sukan zama babban jigo na yaduwar jinyoyi ga mutane sakamakon 'kwayoyin cutar bacteria, fungi, parasite da kuma virus da suke dauke dasu, kamuwar dabbobi da daya daga cikin wadannan 'kwayoyin cutar zaisa ta'ammuli dasu ya zama barazana ga lafiyar dan-Adam, sakamakon zasu iya yada wadannan 'kwayoyinn cutar zuwa ga mutane, ire-iren cututtukan dake yaduwa daga dabbobi zuwa mutane sune ake kira da 'zoonoses' ko kuma 'anthropozoonoses diseases' a turance, kuma ko wane bangare na dabobi (na gida da na daji, manya ko 'kanana) na iya yada jinyoyi ga dan-Adam matukar sun kamu da daya daga cikin wadancan 'kwayoyin cutar da muka ambata.
Hasashen hukumar lafiya ta duniya (WHO) ya nuna cewa Kimanin kaso 61 cikin 100 na jinyoyi ana samun sune daga dabbobi haka zalika kimanin kashi 75 na sababbin jinyoyin dake 'bulla a duniya daga dabobi suke, hakan ke nuna cewa mutane sama da miliyan 50 ke kamuwa da ire-iren jinyoyin da ake samu daga dabbobi a duk shekara kuma a 'kalla mutane sama da mutane 230,000 ke mutuwa a ko wace shekara a duniya sakamakon ta'ammuli da dabobi majinyata.
Ire-iren jinyoyin da mutane kan iya kamuwa dasu daga dabbobi
√ Cutar dake kama da tarin fuka da ake samun ta daga shanu da ake kira da 'Bovine Tuberculosis'
√ Jinyar da ake samu daga jikin mage/kyanwa da ake kira da 'Toxoplasmosis'
√ Jinyar da ake kamuwa da ita ta hangar cizon kare da ake kira da 'Rabies'
√ Jinyar da ake kamuwa da ita ta hanyar 'bera da ake kira da 'Lassa fever'
√ Cututtukan da ake dauka ta hanyar gurbataccen abinci ko abin sha da aka samu 'bullar 'kana nan halittu a ciki da ake kira 'Salmonellosis'
√ Cutar tsutsa da 'karamin hanji ke kamuwa da ita ta hanyar amfani da gurbataccen ruwa da ake kira da 'Ascariasis'
√ Cutar Ebola da ake samu daga jemagu
√ Zazzabin 'zika virus' da ake samu daga cizon wani nau'in sauro da ake kira 'Aedes mosquito'
√ Cutar bacci 'sleeping sickness' da ake kamuwa da ita ta hanyar wani nau'in 'kuda da ake kira 'Tse-tse fly'
√ Jinyar da ake samu ta hanyar cizon kaska da ake kira da 'Lyme disease'
Wadannan kadan ne daga cikin Jinyoyin da ake kamuwa dasu daga dabbobi, a jerin rubuce-rubucen da zamu cigaba da kawo muku akan wannan matsalar zamuyi bayani cikakke akansu daya bayan daya.
Hanyoyin kamuwa da wadannan jinyoyin
Hanyoyin kamuwa da wadannan jinyoyin sun hada da:
√ Mu'amala ta kaitsaye da dabbar da take dauke da 'kwayar cutar bacteria, fungi, parasite da kuma virus da suka hada da:
• Ta'ba abin da ya shafi fitsari, kashi, jini ko yawu na wannan dabbar
• Cizo ko yakushi na dabbar dake dauke da wadancan kwayoyin cutar
√ Mu'amalar da ba takai tsaye ba da majinyatan dabbobi da ya hada da:
• Amfani da kwanon cin abincin dabobin
•Shiga dakin dabobin dake da suke dauke da 'kwayoyin cuta ko kuma barin dabbobin suna yawo a cikin mutane ko kuma suna taba kayan amfanin mutane
√ Ta hanyar 'Kwarin dake daukar cuta su yada irinsu sauro, 'kuda, kaska da sauransu
√ Ta hanyar amfani da nama ko nonon dabbobin dake dauke da jinya a matsayin abinci, ko kuma ta hanyar cin abincin da ya rube ko wanda bai dahu sosai ba da zai haifar da 'bullar wasu 'kananan halittu da zasu cutar da lafiyar dan-Adam.
Hanyoyin kariya daga wadannan jinyoyin
• Rage ta'ammmuli da dabbobin da aka tabbatar da cewa suna dauke da 'kwayoyin cutar da zasu cutar da mutum
• Nisantar cin naman dabbobin da aka tabbatar da cewa suna dauke da jinya
• Kebance dabbobin dake da jinya daga cikin mutane
• Wanke hannu da sabulu yayin da akai ta'ammuli da dabbobi ko kuma yayin da aka shiga wajensu koda ba'a tabasuba
• Kariya daga cizon sauro, kuda ko kaska ta hangar amfani da maganin feshi
• Tabbatar da tsaftar abinci ko abin sha tare da kuma da tsaftar kwanuka, tukwane kafin ayi amfani dasu da kuma bayan angama angama amfani dasu
• Toshe duk wata kafa da 'kananan dabbobi irinsu 'bera zasu shigo cikin gida
• Neman riga kafi kafin kamuwa da jinyoyin da kuma garzawa zuwa asibiti bayan duk wani canji na lafiya da aka ji.
Allah ya 'Kara km karemu
©GHN
Thursday, January 23, 2020
Bayani Akan Illar Yawan shan Maganin Ciwon Jiki ko na Rage jin Radadi (NSAIDs)
![]() |
| Aminu Gambo G. | |
Da yawa mutane a wannan lokacin sun tasirantu da yawan shan magungunan rage ciwon jiki da kuma rage jin radadi duk da cewa magungunan na da matu'kar illa ga dan-Adam, jinsin wadannan magungunan sune ake kira da Nonsteroidal Anti-inflammatory Drugs (NSAIDs) da suka hada da irinsu Feldene, Ibuprofen, Meloxicam, Diclofenac, Indomethacin da kuma Naproxen, haka kuma duk da cewa magungunan suna aikine a jikin mutum ta hanyar dakatar da samuwar sinadarin da ake kira da cyclooxygenase enzymes (Cox-1 & Cox-2) wanda 'kwayar halitta 'cells' ke samarwa, samuwar wannan sinadarin kesa jiki ya iya sarrafa sinadarin 'prostaglandins' dake taimakawa wajen kare ciki daga kwailewa saboda yawan sinadarin sarrafa abinci a ciki, amma kuma duk da haka wadannan magungunan ba sune mafita ga masu fama da ciwon jiki ko jin radadi ba sakamakon manyan illolin da suke haifarwa jikin dan-Adam da suka hada da:
• Haddasa Daskarewar jini tare da haddasa gajiyawar zuciya
• Haddasa Gyambon ciki wato 'Ulcer'
• Lalata Hanta da kuma hana 'koda yin aikin da ya kamata
• Haifar da matsalar 'kwa'kwalwa musamman ga yara 'kanana
• Sannan kuma suna haifar da matsalar Hawan jini da sauransu.
Mafi yawanci ciwon jiki ba jinya bane akaran kansa sai dai yana nuni zuwa ga alamun wata jinyar dake damun mutum, a wasu lokutan kuma ciwon jiki na faruwa ne sakamakon sabanin zaman ƙ'kashi, jijiya da tsoka a jiki, wannan ne ya sa ko da mutum ya sha maganin ciwon jikin da zarar ƙ'karfin maganin ya ƙ'kare a cikin jini sai ciwon ya dawo har sai an 'kara shan wani maganin.
Abin nufi anan shine amfani da wadannan magungunan ba sune hanyar magance matsalar ciwon jiki ba domin basa magance ainahin matsalar da ta haddasa ciwon, saboda matu'kar ba'a daidaita sabanin da ke tsakanin jijiya, ƙ'kashi da tsoka ba to wannan ciwo zai cigabane duk da cewa anashan magani.
Mafita dangane da matsalar ciwon jiki ko jin radadi
• Cire damuwa daga rai da kuma samun ishashen bacci
• 'Kirkirarwa kai nishadi tare da yawan motsa jiki
• Cin abinci mai nagarta
• 'Kauracewa shan ire-iren wadannan magungunan sai idan da sahalewar likita
• Zuwa asibiti lokaci bayan lokaci domin duba ingancin lafiya don samun maganin da yake daidai da bu'katar jikin mutum.
Allah ya 'kara mana lafiya
©GHN
Wednesday, January 22, 2020
Bayani Akan Zazzabin Lassa (Lassa Fever)
![]() |
| Aliyu Abubakar | |
A cikin makon nan ne aka samu 'bullar zazzabin Lassa a jihar kano da yayi sanadiyar mutuwar wasu mutane tare da wasu ma'aikatan lafiya, kasantuwar haka yasa muka kawo muku wannan bayanin domin wayar da kan al'umma akan cutar da kuma hanyoyin da za'abi domin kare kai.
Zazzabin Lassa na daya daga cikin jinsin jinyoyin da ake kira da 'Rodent-borne Hemorrhagic fever' a turance ma'ana jinyoyin da ake dauka daga kananan dabobi irinsu beran gida wato 'Mastomys natalensis' wanda shine kusan ginshiki wajen yada cutar ga mutane sakamakon wata kwayar virus dake da hatsarin gaske da yake dauke ita, mafi yawanci wannan jinya tafi yaduwa a 'kasashen dake yammacin Afrika da kusan kaso 36-67 cikin100.
An fara samun bullar wannan cuta a Nigeria a 'kauyen Lassa dake jihar Borno a shekarar 1969 a wanni sansanin Amurikawa, alkaluman kididdiga na hukumar lafiya ta duniya (WHO) ya nuna cewa kimanin mutane 300,000 dake yammacin Afrika ke kamuwa da zazzabin Lassa a duk shekara kuma a 'kalla mutane 5000 ne ke mutuwa a kowace shekara.
Yadda zazzabin Lassa ke yaduwa
Zazzabin Lassa na yaduwane ta daya daga cikin wadannan hanyoyin:
• Cin abinci ko abin shan da bera yayi kashi ko fitsari aciki
• Sha'kar iskar da take gurnace da kashi ko fitsarin bera
• Cin naman beran dake dauke da wannan 'kwayar cutar
• Taba yawu, jini ko majina na mutumin da jinyar ta baiyana a jikinsa, amma indan alamun basu baiyana ba to taba wadannan abubuwan baza susa mutum ya kamu da jinyarba, haka kuma mu'amalar jiki da jiki da mai jinyar irinsu gaisuwa ko runguma basa sa a kamu da jinyar.
Alamomin zazzabin Lassa
'Kwayar cutar zazzabin Lassa na iya ratsa ko ina a jikin dan-Adam, Alamun na fara baiyana ne bayan sati 1-3 da kamuwa da 'kwayar cutar, alamomin cutar sun kasance kamar haka:
√ Mataki na farko wanda shine ke dauke da kusan kaso 80 cikin 100 na alamun jinyar ya hada da tsananin zafin jiki, tsanin gajiya da kuma tsananin ciwon kai.
√ Mataki na biyu shine ya dauki kusan kaso 20 cikin 100 na alamun jinyar Wanda ya hada da ciwon jiki, kurajen jiki da na baki, lalacewar koda ko zuciya, amai, ciwon baya da na kirji, shan numfashi da kyar, ciwon ciki da kuma gudawa mai jini aciki a wasu lokutan mutum na iya rasa jinsa.
√ Mataki na uku shike dauke da kaso 15 cikin 100 na alamun jinyar wanda ya hada da kumburin fuska sai kuma zubar jini ta baki, hanci da kuma farji ga mata, mafi ya wanci ba'a cika rayuwa ba idan akazo wannan matakin, da zarar mutum ya fara jin days daga cikin alamomin da muka ambata a matakin farko da ya garzaya zuwa asibiti domin daukar matakin gaggawa.
Hanyoyin kariya daga zazzabin Lassa
Matakan kariya daga zazzabin Lassa sune kamar haka:
√ Mataki na farko ya hada da matakan kariya da ake bi Kafin akamu da jinyar wanda suka hada da:
• Kula da tsaftar muhalli
• Kora ko toshe duk wata hanyar shigar bera gidajenmu
• A daina barin abinci ko kwanuka a bude idan dare yayi
• Rufe hanci da kyalle yayin da ake share kashin bera ko fitsarinsa
• Zuwa asibiti da zarar zazzabi ya wuce kwana biyu
√ Mataki na biyu ya hada da matakan da ake bi bayan kamuwa da jinyar wanda suka hada da shan maganin dake kashe kwayar cutar virus wato (antiviral drugs) irinsu Ribavirin dasauransu.
Allah ya 'Kara karemu.
©GHN
Monday, January 20, 2020
Bayani Akan Kansar Bakin Mahaifa (Cervical Cancer)
![]() |
| Aliyu Abubakar | |
Kansar bakin mahaifa dayace daga cikin nau'inkan kansa da take da hatsari ga mata bayan kansar mama (breast cancer), alkaluman 'kididdiga na cibiyar kula da lafiya ta duniya wato (WHO) da kuma cibiyar bincike akan cutar kansa ta duniya wato (IARC) sun nuna cewa kimanin mata 570,000 ne ke dauke da wannan cuta a aduniya, kuma cutar na kashe mata fiye da 311,000 a kowace shekara, kimanin kashi 87 cikin 100 na cutar na kama mata ne a kasashe masu tasowa irin Najeriya; duk da cewa ana iya shawo man cutar cikin sauki.
Cibiyar kula da lafiyar iyali ta Society for Family Health (SFH) tace a Nigeria akalla kimanin mata sama da 10,000 ne ke rasa rayuwarsu duk shekara sanadiyar wannan cuta, kuma mafi yawancin matan da sukafi fama da wannan cuta daga yankin arewacin kasar suke.
Yadda mata ke kamuwa da kansar bakin mahaifa
Ana kamuwa ne da wannan cutane ta hanyayar wata 'kwayar cutar virus mai suna Human Papiloma virus (HPV), Kuma mafi yawanci cutar na ya duwane ta hanyar jima'i, duk da cewa da yawa wadanda ke dauke da wannan 'kwayar cutar basu san suna dauke da itaba, cutar na kasancewa tare da matane sanadiyar yawan aurace-aurace, yawan haihuwa da kuma saduwa da matan dake da shekaru kadan.
Yadda abin yake faruwa shine ita 'kwayar cutar 'HPV' na zuwa ta sa jinya a wuyan mahaifa (cervix), jinyar bazata dadeba a wuyan mahaifar saboda cikin gaggawa garkuwar jiki zata yaketa, sai dai inda matsalar take dazarar wannan jinyar ta shiga wuyan mahaifa take canza kwayoyin halittar wajen wato (cells) zuwa wani yanayi na sharar fagen kamuwa da kansa (pre-cancer cells), duk da cewa kwayoyin halittar (cells) na iya dawowa daidai yadda suke koda kuwa ana kan wannan matakin idan har an gano matsalar da wuri an kuma maganceta, idan har ba'a gano matsalarba to wadannan 'kwayoyin halittar da suke matakin sharar fage na zama kansa to zasu koma su zama 'kwayoyin halittar kansa (cancer cells) kai tsaye.
Alamomin kamuwa da kansar bakin mahaifa
Babu wata alama da ake iya gane cutar kansar baking mahaifa a karon farko, mafi yawanci dai ana iya gane alamun cutan ne a lokacin da ta tayi nisa a jikin macen da shekarunta suka gota 30, daga cikin alamomin cutar da aka fi gani sun hada da:
• Zuban jini a gun mace da ta gama al'adar ta
• Zuban jini yayin saduwa da miji
• Zuban jini tsakanin al'ada (period) zuwa wata
• Fitar ruwa mai wari daga gaban mace
Hanyoyin kariya daga cutar kansar bakin mahaifa
Ana samun kariya daga cutar kansar bakin mahaifa ta wadannan hanyoyin:
• Rigakafi: Ana samun kariya daga cutar kansar mahaifa ta hanyar yin allurar rigakafin kwayar cutar Human Papiloma Virus (HPV) ga yara mata 'yan shekara 9-13 kafin su fara mu'amala da maza.
• Gwajin bakin mahaifa (Pap Smear Test): Wannan gwajin anayinsane dan gano alamar kansar bakin mahaifa tun kafin ta zama kansa, ana bukatar mata 'yan shekara 21 zuwa sama dasu maida hankali wajen ganin ana musu wannan gwajin domin samun tabbaci akan cewa suna dauke da alamun wannan cuta ko kuma basa dauke da ita, akalla duk bayan shekara 3 anaso a sake maimaita gwajin.
Banda Pap smear test akwai wasu gwaje-gwajen da ake amfani dasu wajen gano wannan cuta irinsu HPV test da VIA screening, domin tabbar da jinyar shi zaisa adauki matakin kariya na gaggawa daga jinyar, da fatan za'a dinga tuntubar likitoci kwararru akan matsalolin lafiya gaba daya.
Daga yau 21st -27th January, 2020 zaku iya turo mana da tambayoyinku akan wannan cutar musamman 'yan uwa mata, domin a shirye muke domin amsa tambayoyinku, Allah ya Kara mana lafiya.
#WayarDaKai
#MuYakiKansarMahaifa
#CervicalCancerAwarenessWeek
#Jan_2020
©GHN
Sunday, January 19, 2020
Bayani Akan Ciwon Olsa (Peptic Ulcers)
Nuraddeen Abba Mustapha | |
Ciwon Olsa (Peptic Ulcers) daya ce daga cikin ciwuka da dake addabar sashen da ya shafi ciki da ake kira da (gastrointestinal tract) a turance, mafi ya wanci akan kira olsa da gyambon ciki sakamakon tafi kama tumbi, karamin hanji da kuma kwararon ma'kogoro wato (Oesophagus).
Yadda Ciwon Olsa ke faruwa
Ciwon olsa na faruwa ne yayinda bangon kariya wato (gastrointestinal barrier) da ya katange sassan hanji ko tumbi ya samu rauni ko ya kuje, amfanin wannan bangon kariyar shine bada kariya ga kafofin jini na jiki daga dukkanin wani abu da yake a cikin tumbi ko hanji.
Abubuwan da suke kawo Ciwon Olsa
√ 'Konewar sinadarin Hydrochloric acid wanda ake samarwa a tumbi don narkar da abinci, 'konewar wannan sinadarin shi kesa bangon kariya na tumbi ko hanji ya sami rauni
√ Kamuwa da 'kwayar cutar Bakteriya da ake kira da Helicobacter pylori (H pylori)
√ Yawan amfani da nau'ikan magungunan rage jin zafi ko zugi da ake kira Non-steroidal anti-inflammatory drugs (NSAID) irinsu Diclofenac, Ibuprofen dasauransu, cikakken bayani zaizo a rubutun mu na gaba kan illolin amfani da wadannan magungunan
√ Yawan ci ko shan abubuwan da suke 'kunshe da sinadarin caffeine acikinsu da ya wuce kimanin >400mg a rana
√ Shan Barasa
√ Damuwa mai tsanani
√ Rashin cin abinci akan lokaci musamman Karin safe
√ Cin abincin da yake da mai'ko ko abin sha mai tsami sosai
Abubuwan da muka ambata asama na farko da na biyu Kai tsaye suna samar da rauni/ciwo ga bangon kariya ta hanyar rarake kariyar (barrier), Sauran abubuwan kuma suna haifar da Ciwon Olsa ne ta wata hanyar daban wadda ta shafi sinadarai na jiki.
Alamomin ciwon olsa
√ Yawan jin Amai
√ Rashin sha'awar abinci
√ 'Kuna a 'kirji ko zafin ciki
√ Fitar da jini daga tumbi ko hanji
√ Yawan gyatsa, magwas, da kuma danka ko kumburin ciki
√ Ramewa ta rashin dalili
√ Ciwo ta 'bangaren baya musamman yayin cin abinci
Hanyoyin Kariya daga Ciwon Olsa
√ Rage yawan amfani da kayayyakin 'kanshi ko yaji a abinci domin suna dauke da sinadarin dake faama ciwo da ake kira da Capsiasin
√ Daina shan Taba Sigari da kuma Barasa, tare da Nisantar abubuwan dasuke 'kunshe da sinadarin caffeine a ciki
√ Cin abincin da ya hada da ganyayyaki da kuma kayan marmari.
Kiyaye wadannan matakan da muka ambata na kariya na taimakawa wajen rage kamuwa da Ciwon Olsa.
Magungunan Ciwon Olsa
Ciwon olsa akan iya maganceshi ta hanyoyi da dama mafi sauki shine ta hanyar shan magunguna, Magunguna olsa ana amfani da sune kawai bayan rubutawar likita idan aka yi gwajin ciwon olsa akan mara lafiya kuma aka tabbatar da cutar ta hanyoyi da dama da suka hada da gwajin da da ake haska cikin mutum wato Endoscopy/Gastroscopy da kuma gwajin kwayar Bacteriya ta H pylori da ake amfani da Jini ko Bahaya na mutum da dai sauransu.
Magungunan magance Ciwon Olsa sun hada da:
√ Nau'in maganin da ake kira da Antibiotics: Idan akayiwa mutum gwajin jini ko bahaya na kwayar bacteriyar H pylori sakamakon gwajin ya nuna cewa akwai samuwar wannan 'kwayar bacteriyar dake sa ciwon olsa, za ayi amfani da a 'kalla kala biyu na wannan jinsin maganin da suka hada da; Tetracycline, Metronidazo, Amoxicillin, clarithromycin, za ayi amfani dasu sau biyu a rana na tsahon sati biyu domin kashe 'Kwayar cutar.
√ Magungunan rage yawan sinadarin narkar da abinci da jiki yake samarwa wato (Hydrochloric acid) wanda suka hada da:
• Nau'in maganin da ake kira da Proton pump blockers (PPIs) irinsu Omeprazole, Pantoprazole, Lansoprazole
• Nau'in maganin da ake kira da Antihistamine drugs/H2-receptor antagonists irinsu Cimetidine , Ranitidine, Nizatidine
• Nau'in maganin da ake kira da Mucous lining protectors irinsu Sucralfate ( carafate)
• Nau'in maganin da ake kira da Mucus and HC03 producing drugs irinsu misoprostol
• Nau'in maganin da ake kira da Antacids irinsu Gestid, Gelusil da kuma nau'in maganin da ake kira Alginates da sauransu. A takaice mai ciwon olsa akan dorashi akan tsarin da ake kira da Triple Therapy ma'ana zaiyi amfani da magani kala uku alokaci daya biyu daga ciki zasu yaki 'kwayar bakteriyar H pylori dayan kuma zai hana fitowar sinadarin Hydrochloric acid daga jiki, shan wadannan magungunan daidai da yadda likita ya tsara zai taimaka wajen rabuwa da jinyar.
Shan maganin rage jin radadi ko zugi wato (NSAID) kamar yadda muka ambata a baya na daga cikin nau'ikan magungunan dake haifar da ciwon olsa saidai idan ya zama ba makawa sai anyi amfani dasu to a iya amfani da wadanda suke da dama-dama cikinsu da ake kira da COX-2 inhibitor irinsu Celebrex, kuma ana iya amfani da Paracetamol domin rage zafin radadin ciwon olsa.
Ginsau HealthNetwork a shirye suke domin amsa tambayoyin ku ko baku shawarwari da suka shafi ingancin lafiyarku, muna rokon Allah daya 'karamana lafiya.
Mungode
©GHN
Subscribe to:
Comments (Atom)






